Manyan Labarai Guda 8 Da Sukayi Fice A Ranar Laraba 13 Ga Watan Agusta

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

19 people like this topic, 36 people dislike this topic

Abiodun
Posts: 0
Joined: Mon Sep 29, 2014 10:22 pm

Manyan Labarai Guda 8 Da Sukayi Fice A Ranar Laraba 13 Ga Watan Agusta

Postby Abiodun » Thu Aug 13, 2015 2:20 pm

WikiNaira.com ta tattara maku manyan labarai guda 8 da sukayi fice a ranar Laraba 8 ga watan Agusta. Ku duba domin Ku same su.


1. Boko Haram ta samu sabon shugaba – Derby.


Shugaban Kasar Chadi  Idris Derby ya bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta samu sabon shugaba saboda mutuwar Shekau. Sabon shugaban kuma shirye yake da yayi sulhu.


2. Binne Sarkin Ife ya tsaya.


Abobaku wanda za’a binne shi da Sarkin Ife ya ruga. Wannan na nuna cewa binne mataccen sarki an dakatar dashi.


3. Buhari zaya bayyana mukarraban gwamnatin shi nan bada dadewa na – Oyegun.


Shugaban jam’iyyar APC ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zaya nada mukaraban gwamnatin shi nan bada dadewa ba.


4. Helikwaftan Bristow ya fadi a Legas.


Wani Helikwafta na Bristow helicopters daya taso daga fatakwal ya fadi a tamfkin Oworosoki dake Legas da kimanin karfe 3 na rana. Helikwaftan dai na dauke ne da mutane 12.

5. Wasu kungiyoyi sun kai Fashola kara wajen Hukumar EFCC.


Wasu kungiyoyi guda 5 dake Legas  sun kai tsohon gwamnan jihar Legas kara zuwa wajen hukumar hana almundahana ta Kasa. Sun bayyana cewa wasu kudade daya kashe nada alamar tambaya.


6. Buhari ya canza daga yadda yake a can baya – Soyinka.


  Mai rike da kambin Novel Wale Soyinka ya bayyana cewa shugaba Buhari ya canza daga yadda yake a can bayan.


7. An buga ma perterside Dakuku, Magnus Abe barkonan tsohuwa a ofishin zabe ta Kasa dake Abuja.


  An buga ma dan takarar jam’iyyar APC Daktar Peterside Dakuku barkonan tsohuwa a ofishin hukumar zabe dake a Abuja kuma aka hana shi Shiga.


8. Hukumar gudanar da jarabawar WAEC tace zata saki sakamakon jarrabawotin data rike.


Hukumar gudanarwa ta jarabawar WAEC ta bayyana cewa zata saki Sakamokon jarabawoyin data rike ciki sa’o’i 24.


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.


 


Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 2 guests

cron