Page 1 of 1

Sojojin Najeriya Na Kara Damara Wajen Yakar Boko Haram

Posted: Fri Aug 14, 2015 1:43 am
by tola
Sojojin Najeriya zasu kara himma wajen yakar yan Boko Haram musamman yanzu da suka sake himmar  wajen kai hare-hare a Arewacin Najeriya. Jami’i mai kula da labarai na Hedikwatar sojojin kasa, Kanar Rabe Abubakar ne ya bayyana hakan.

details

Abubakar ya bada tabbacin jajircewa sojojin Najeriya wajen Kawo karshen yan Boko Haram inda ya masilta su da ”gidadawa.” Sannan kuma ya nuna bacin ranshi akan yadda suka kashe mutane da yawa tunda suka fara tada kayar baya.

Yace: “Muna daukar matakai daya bayan daya domin kawo karshen yan Boko Haram. Yanzu karfinsu ya rage sosai kuma basu iya fuskantar sojojin Najeriya. Matsugunnan da suke zaune ma duk sun gudu sun bar su,” cewar Jami’in.

Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.

 

Re: Sojojin Najeriya Na Kara Damara Wajen Yakar Boko Haram

Posted: Thu Mar 17, 2016 3:05 pm
by personpikin
Good