'Za a kafa sansanoni ga mutanen Gwoza da Bama da Konduga'

Discussion Board for Hausa News, Hausa Music,Hausa Language, Poetry and Prose here.

24 people like this topic, 29 people dislike this topic

User avatar
wikinaira
Posts: 2454
Joined: Mon Sep 10, 2012 3:44 pm

'Za a kafa sansanoni ga mutanen Gwoza da Bama da Konduga'

Postby wikinaira » Sat Aug 15, 2015 1:21 pm


Mutane fiye da miliyan ne suka fice daga muhallansu saboda rikicin Boko Haram

Rundunar sojin Nigeria ta ce ba ta bukaci al'ummar kananan hukumomi uku na jihar Borno, da suka gujewa rikicin Boko Haram su koma gidajensu.


Rundunar ta ce za ta kafa sansanonin 'yan gudun hijira ne a kananan hukumomin Bama da Konduga da kuma Gwoza domin rage matsatsin da ake fuskanta a Maiduguri

Kakakin rundunar soji a Maiduguri, Kanar Tukur Gusau ya shaidawa BBC cewar za a kafa karin sansanoni ne a wadannan wuraren domin rage kunci da 'yan gudun hijira ke fuskanta a Maiduguri.

A shekarar da ta wuce kungiyar Boko Haram ta kwace iko da garuruwa da dama a jihohin Borno da Yobe da Adamawa inda ta yi ikirarin kafa daular Musulunci.

'Hadin Gwiwa'

A farkon wannan shekarar dakarun Nigeria tare da hadin gwiwar na wasu makwabtan kasashe suka kwato garuruwan da hannun 'yan Boko Haram inda suka fatattaki mayakan kungiyar.

Tun da aka rantsar da Buhari a matsayin shugaban Nigeria a karshen watan Mayu, kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane kusan 900.

A karshen watan Yuli ne rundunar hadin gwiwa kan yaki da Boko Haram mai dakaru 8,700 ta soma aiki.

Rundunar ta kunshi sojoji daga Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma jamhuriyar Benin.I don't try to make my presence to be noticed, I only strive to make my absence to be felt http://www.wikinaira.com

Return to “Hausa”

Who is online

Users browsing this forum: No registered users and 1 guest

cron